Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar ta na ci gaba da shirye-shirye na musamman don ganin 'yan gudun hijara sun kada kuri’a a zaben 2023.
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP a Najeriya wanda ya yi murabus ya ce ya ajiye mukamin sa ne don samun sulhu a jam’iyyar, bisa korafin yawan mukamai a yankin arewacin kasar.
A kwanakin baya, rahotanni sun yi nuni da cewa Walid Jibrin da kansa ya fito ya ce bai dace a ce dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya su fito daga yanki daya ba.
Yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke kokarin ganin ta ci gaba da zama a kan karagar mulki, ita kuwa PDP kokari take ta ga mulkin ya dawo hannunta.
Dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa sanata Kashim Shattima sun sha alwashin bai wa mata sama da kaso 35 cikin 100 na damarmaki da mukamai idan har suka sami nasara a zaben shekarar 2023.
Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba? Ga abinda Kwankwaso ke cewa. (An buga asali a ranar 8 ga Agusta, 2022)
Yayin da bangarori daban daban na hukumomin Najeriya ke kintsawa don tinkarar babban zaben Najeriya na 2023, su ma 'yan sanda ba a bar su a baya ba.
Domin Kari