Mataimakiyar shugabar matan jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa, Mal. Zainab Ibrahim, ce ta bayyana hakan a yayin taron kaddamar da shirin nan na shugabanin majalisun dokokin jihohin arewa na tallata yan takarar jami’yyarsu ta APC, wato Bola Tinubu da Kashim Shattima ga masu kada kuri’a a game da zaben shekarar 2023 zuwa gida-gida a yayin da ake daf da fara gangamin yakin neman zabe a hukumance.
A game da wannan taro, Mal. Zainab ta kara da cewa sun fara bi gida-gida domin tabbatar da cewa mata sun mallaki katin zaben su tare da wayar da kan su a kan mahimmancin kar su yadda su sayar da katin zaben na dindindin.
Shugabannin majalisun dokokin jihohi karkashin inuwar jam’iyyar APC ne suka hada taron wanda ya sami halartar akasarinsu daga jihohin arewa don nuna goyon baya ga Tinubu da Shattima a yayin da jamiyyu ke shirin fara gangamin yakin neman zabe gadan-gadan kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna, a cewar kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji İdris Garba.
A yayin jawabinsa a lokacin taron, mataimakin dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shattima ya mika godiya ga shugabannin na majalisun jihohin arewacin kasar da suka shirya taron tare da yaba musu a kan jajircewa da rike amana da kuma jagoranci nagari da suke yi. Ya kara da cewa idan APC ta kafa gwamnati a shekarar 2023 zasu hada gwiwa don kawo ci gaba a kasar.
A bisa jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, a ranar 20 ga watan Satumbar da muke ciki ne zata buga jerin ƙarshe na sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, sai kuma na yan takarar gwamnoni da yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, a ranar 4 ga watan Oktobar mai zuwa don al’umma su shaida.
Haka kuma, ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyu daban-daban su fara gangamin yakin neman zabe a bainar jama’a a ranar 28 ga watan Satumbar nan, sai ‘yan takarar gwamnoni da majalisun dokokin jihohi su fara nasu a ranar 12 ga watan Oktoba mai zuwa.
A saurari labari cikin sauti.