Alkaluman da hukumomi suka fitar a karshen makon nan a Najeriya sun nuna cewa kasar ta fita daga tawayar tattalin arzikin da take fuskanta.
Kungiyar Cinikayya ta Duniya ta fitar da wani faifan bidiyo da nufin gabatar da sabuwar shugabar da aka zaba yau.
Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) ta tabbatar da zaben tsohuwar minister kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar, da kawo karshen jan kafa da aka yin a tsawon watanni a cike gurbin babban darektan kungiyar da ke da shalkwata a Geneva.
Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga gwamnonin yankin da su samawa makiyaya matsuguni sakamakon yadda aka bada wa’adin su fice daga wasu sassan Najeriya.
Tun bayan da aka fara zanga zanga a Myanmar kan juyin mulkin da sojoji suka yi, ma’aikatan lafiya sun bi sahun masu wannan bore wajen nuna adawarsu da matakin sojin.
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF, ta shawarci gwamnatin Najeriya ta kara kudaden harajinta na VAT daga kashi bakwai da rabi cikin dari zuwa kashi goma cikin dari nan da shekara daya.
Kungiyar manoma da masu sarrafa masara da sayar da ita a Najeriya ta bayyana cewa tana da isassun masarar da za ta wadaci al’ummar kasar a wannan shekarar duk kuwa da kalubalen da annobar Coronavirus ta kawo ga harkokin noma a kasar.
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta ce kimanin kashi 15-20% na Fulani makiyaya na Najeriya na ficewa daga kasar zuwa tudun mun tsira.
A karon farko gwamnatin tarrayar Najeriya ta kaddamar da motoci da ke amfani da wutar lantarki a maimakon man fetur, hakan na zuwa ne Karkashin hukumar da ke sa ido wajen ci gaba da zane-zanen motoci ta kasar wato NADDC.
Tsohuwar Ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweal, na shirin zama mace ta farko kuma ‘yan nahiyar afrika ta farko, da za ta shugabancin kungiyar hadahadar kasuwancin duniya WTO.
Hukumar hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya NITDA, da hadin gwiwar ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, ta kaddamar da aikin gina cibiyar kere-keren fasahohin zamani da kasuwanci.
A daidai lokacin da matsin lamba ke kara yawaita a kan fulani makiyaya su fice daga kudancin Najeriya, ‘yan arewa sun ce ai dama sakacin gwamnatoci ne ya kawo hakan domin arewa ta wuce ayi mata gori da fadin kasa mai dausayi da tsiro wadda kan iya wadatar da makiyaya.
Domin Kari
No media source currently available