Daukacin hadahadar da aka yi a kasuwar ta kare da maki 40,186.70 a harshen makon.
An dai juya hannayen jari da yawansu ya kai biliyan 1.54 akan kudi Naira biliyan 18.24 in hada-hada dubu 22,752 da aka yi a makon da ya gabata a zauren kasuwar hannayen jarin.
Haka ya yi hannun riga da hannayen jarin da aka juya biliyan 2.68 aka juya akan kudi Naira biliyan 26.66 a hada-hada 27,844 da aka yi a wancan makon d aya gabata.
Sashen hada-hadra kudade ne aka fi juya kudade da hannayen jari biliyan 1.09 da aka yi wa kudi Naira biliyan 11.11 a cinikayya 12,544 da aka yi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Cinikayyar wannan fanni ta ba da gudunmowar kashi 71.35 a daukacin cinikayyar da aka yi.
Sai bangaren kayayyakin amfani wanda aka juya hannayen jari miliyan 133.16 wadanda kudadensu suka kai Naira biliyan 2.33 a cikin cinikayya 3,941 da aka yi.