A yan Kwanakin nan ne Majalisar zartarwar hukumar kasuwancin ta duniya ta zabi Ngozi Okonjo-Iweala, bakar fata kuma yar Nahiyar Afirka ta farko da ta taba rike mukamin tsohuwar ministar kudi ta Najeriya sau biyu a Matasayin babban daraktar hukumar ta 7.
Bayan samun nasara da ta yi a matsayin babbar daraktar hukumar, Okonjo-Iweala ta bayyana tsare-tsaren ta da suka hada da yin aiki tare da sauran mambobin hukumar wajen sauya fasali da canja tsarin hukumar kasuwancin Ta duniya.
A jawabin ta na karbar aiki, Okonjo-Iweala, ta ayyana bukatar bin ka’idojin tsare-tsaren hukumar saboda ta samu biyan bukatun dukannin mambobinta.
Okon ji-Iweala za ta iya sabunta wa’adin jagorancin ta da zai kare a hukumance a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2025.
A cewar ta, kundin tsarin jagorancin hukumar kasuwancin dake da mazauni a birnin Geneva, na bukatar gyara sakamakon yadda wasu manufofinta musamman yarjejeniyoyin kasa-da-kasa na wasu shiyoyi wanda su ke shigar da wasu kera-Keren zamani.
Okonjo-Iweala ta jadada bukatar sabunta wannan kundin jagoranci don shiga a dama da hukumar a wannan karnin na 21 kamar kasuwancin zamani ta yanar gizo, da tattalin arziki na fasahar zamani, wand ta ce ya dauki tsawon lokaci cikin yanayi na rashin tabbas.
Saboda haka ta ce "amma lokaci ya yi, sabuwar rana ta zo, kuma aiki zai fara gadan-gadan a zahiri."