Nadin na zuwa ne yayin da sabuwar gwammatin ta Biden take ci gaba da cike guraban shugabancin hukumomi da ma’aikatun kasar.
“Abin alfahari ne dawowa wannan ma’aikata ta USTDA don jagorantar ta a daidai wannan lokaci mai muhimmanci – lokaci da idon duniya ke kan Amurka wajen ganin ta jagoranci tafiyar samar da tsabtataccen makamashi.” In ji Ebong.
Ebong ta taba aiki a wannan ma’aikatar daga 2004 zuwa 2019. Ta girma a birnin Legas da ke kudancin Najeriya, kafin daga bisani ta yi kaura zuwa Amurka.
A baya ta rike mukamai daban-daban a a’aikatar, na karshe shi ne mukamin babbar lauyar ma’aikatar da ta rike.
Kafin wannan nadi, ita ce shugabar cibiyar kulla huldar cinikayya ta Miken Centre da ke fadada muradun Amurka ta fannin cinikayya.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya taya Enoh Ebong murnar zama shugabar wannan ma’aikatar.
Ma’aikatar ta USTDA, wacce aka kafa ta a shekarar 1992, ita ke da alhakin ganin tattalin arzikin Amurka ya bunaksa tare da kare muradun harkokin kasuwancin kasa a kasashen masu tasowa.
Ebonng ta yi karatu a Jami’ar Michigan inda ta karanci aikin lauya, tana da digiri na biyu a fannin ilimin sadarwa a jami’ar Pennsylavania da kuma wani digiri na biyu fannin tarihi a jami’ar Edinburgh, Scotland.