Daruruwan ‘yan adaidaita sahu ne suka shafe kwanaki uku suna gudanar da zanga zangar lumana a jihar Kano, dangane da harajin Naira dari-dari da hukumar karba haraji ta ce su biya.
Adaidaita sahu dai shine hanya mafi sauki na gudanar da sufuri a jihar Kano da ma wasu sassan Najeriya, wanda da shi ne mafi yawan al’umma suke zirga zirga na yau da kullum.
Musbahu Lawal Ahmad dan adaidaita sahu ne da ke Kano ya ce wannan doka sun san da ita amma a da naira hamsin-hamsin suke biya sannan da zarar ka je biya sai a ce sai sun biya na wata shida ko na shekara daya, kuma dole sai dan adaidaita ya karbi remita.
Sannan a ce a dole sai ka biya na watanni kuma idan aka yi lissafi kudin suna da yawa.
Shi kuwa Ayuba Ibrahim Saraki cewa ya yi da suna biyan naira hamsin-hamsin, a wannan lokaci abin da ya sa suka gudanar da zanga zanga an ce dole sai sun biya na wata shida ko shekara.
Saraki ya kara da cewa ya dace a samar musu wata hanya mafi sauki na biyan kudin sannan kuma lokaci da aka basu kalilan ne.
Matsayin Hukumar KAROTA
Shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce ba guda ba ja da baya wajen karbar haraji daga wajen ‘yan adaidaita sahu a jihar Kano.
Ya ce kamar yadda hukumar karbar haraji ta gindaya na karbar haraji a wajen masu ababan hawa, ciki har da adaidaita sahu na biyan harajin naira dari-dari ga dukkanin mai abin hawa dama yana cikin doka ba wani sabon abu bane.
Baffa ya kuma kara da cewa gwamna ya dagawa masu ababan hawa kafa ne a bara sakamakon cutar COVID-19, wanda tuni wasu suka biya na shekara guda, wanda a yanzu an shigo sabuwar shekara dole a biya na sabuwar shekara.
Ya ce yayi mamaki da wasu ‘yan adaidaita sahu suka shiga kafafan yada labarai suna korafi, kafin a fara wannan batu sai da aka sanar da su wannan al’amari.
“Masu ababan hawa zasu iya biyan wannan kudi na haraji ne a hukumar karbar haraji ko na wata daya ko na shekara guda, aikin hukumar karato dai shine tabbatar da cewar kowa ya biya haraji, rashin biyan wannan kudi idan an kama mai laifi zai biya tara bayan ya biya kudin harajin,” a cewar Baffa.
Kudin harajin dai da shi ake aikace aikacen gyaran tituna da sauran ayyukan ci gaban kasa.
Baffa ya kara da cwae zanga-zangar da ‘yan adaidaita sahu suka gudanar domin tada zaune tsaye ne, sannan wannan haraji a banki ake biya ba wai a hannu ake biya ba.
Kawo yanzu sama da mutane 500 suka yi rijista domin biyan kudaden harajin adaidaita sahun su.