Kungiyar makiyaya a Najeriya ta Miyetti Allah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wani shirin bada taimako ga makiyayan domin rage musu radadin asarar da suke yi na dabbobin su a fadin Najeriya lamarin dake jefa su cikin kuncin rayuwa.
‘Yan kasuwa na kokawa kan rufe kasuwar Wuse, Abuja sakamakon yadda wasu ’yan kasuwa suka ki mutunta ka’idojin kare kai daga Coronavirus.
A Jamhuriyar Nijer an bude bikin kaddamar da wata cibiyar kasuwancin albasa a birnin Yamai da nufin karfafa hanyoyin baiwa manoman albasa da masu kasuwancinta damar cin moriyar wannan sana’a.
Ana sa ran samar da karin allurar riga-kafin cutar COVID-19 zai taimaka wajen farfado da karfin tattalin arzikin duniya a wannan shekara, a cewar wani hasashe da hukumar ba da lumani ta IMF ta yi a ranar Talata.
Hukumar kula da hakkoki da karfafa gwiwar ‘yan kasa akan harkokin albarkatun mai da Iskar gas ta Najeriya ta ce damar da kamfanonin cikin gida masu hada-hada a bangaren albarkatun mai na kasar sun karu da kimanin kashi 30 cikin dari.
Duba da irin alfanun da albasa ke da shi a jikin bil'adama da kuma irin tashin gwauron zabi da farashinta ya yi a Najeriya, wanda ba a taba gannin irinsa ba a tsawon lokaci ya sa aka kafa sabuwar kungiyar ‘yan kasuwa ta masu sarrafa albasa ta kasa.
A ranar Litinin hukumomi a kasar Italiya sun ci tarar kamfanin Apple Euro miliyan 10, kimanin dala miliyan 12.
Nan ba da jimawa ba, kasar mu zata shiga jerin kasashen da suka cigaba a fanin kimiyya da fasahar zamani.
Sudan Ta Kudu za ta haramta amfani da kudaden kasashen waje a kasar, a zaman hanyar magancen tabarbarewar tattalin arziki da tashin farashin kayan masarufi.
Neman sinadaran kariya daga cututtuka, a wannan marra ta annobar corana, ya sa an shiga ribibin citta a kasuwannin duniya, wanda hakan na amfanar Najeriya.
Kamfanin sadarwar MTN a Najeriya ta fara gwajin amfani da wayoyin hannu marasa katin sim a wani kokarin jagorantar canjin da inganta kwarewar sadarwar zamani.
Domin Kari
No media source currently available