A cewar Farfesa Danbatta, sarrafa ilimin ta yin shi a aikace ta hanyar da ta dace, zai taimakawa matasa wajen samun ayyukan da za su rage dogaron da suke yi da ayyukan gwamnati.
Elon Musk dan kasar Amurka, shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a duniya inda ya mallaki dala biliyan 194.
Bankin na CBN ya kuma ce zai dakatar da ayyukan ba da lasisi ga masu neman bude kasuwancin canjin kudaden kasashen waje.
Hakan na nufin idan an kammala aikin, za a samu hanyar sufurin jirgin kasa tun daga Abuja har zuwa Kano.
A farkon makon nan kungiyar ta IPOB ta yi yakuwar mambobinta ta kauracewa kayayyakin kasar na Kenya saboda rawar da ta zarge ta da taka wa wajen kama Nnamdi Kanu.
A Jamhuriyar Nijar masu sarrafa kayan noma da kiyo sun fara gudanar da taro domin tsayar da shawarwarin da za su gabatar a taron hukumar cimaka na birnin Roma da taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a kowane watan Satumba a birnin New York.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramta amfani da mutum mutumi ga Masu shagunan sayar da kaya da teloli, inda ta ce yin haka ya sabawa addinin musulunci.
Rahoton hukumar bincike da kididdiga ta Najeriya, ya bayyana cewa adadin bashin da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar ya kai naira tiriliyan 33.11 ya zuwa 31 ga watan Maris.
A cewar Akinwumi, gabanin barkewar annobar, akwai kasashe 6 a nahiyar da tattalin arzikinsu ya hau turbar zama tattalin arzikin da ke bunkasa a duniya.
Daga cikin kayan da aka baje, har da mota kirar Hyundai Kona mai amfani da wutar lantarki, wacce aka hada sassanta a cikin kasar.
Hukumomin kasar sun ce sun rufe kafar sada zumuntar ce, saboda tana barazana ga zaman lafiyar Najeriyar, la'akkari da irin sakonnin da take bari ana wallafawa.
A kwanakin baya hukumomin kasar suka bayyana cewa, Najeriyar na shirin kaddamar da waya wacce aka kera a kasar hade da katin waya na sim.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.