Ministan lamurran ci gaban matasa da wasanni na Najeriya Sunday Akin Dare ya kaddamar da wani sabon shirin samar da ayyukan yi ga matasa na shekarar 2021 zuwa 2024 a Abuja.
Ministan ya ce kaddamar da shirin yana nuni da jajircewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da ayukan yi har miliyan 3.7 a duk shekara, da kuma cimma muradun ci gaban kasa, musamman ta fannin tattalin arziki mai dorewa.
"Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta yi amfani da karfin yawa da kwazo- matasa wajen rage hasturan matsalar tsaro a kasa," in ji minista Dare.
Ya kuma kara da cewa kamata a yi amfani da matasa a matsayin jarin da kan iya samar da ci gaban tattalin arzikin al’umma, a maimakon ba su wasu kananan ayyuka lokaci zuwa lokaci.
Ministan ya bayyana takaicinsa dangane da matsalar rashin ayukan yi da matasa a kasar ke fama da shi, inda ya ce tasirin matsalar bai tsaya a bangaren matasan kadai ba har da matsalar talauci da koma baya da kasar ke fuskanta.