Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lagos Na Shirye-shiryen Bude Kasuwar Baje Koli


Jihar Legas a Najeriya
Jihar Legas a Najeriya

Hukumomin jihar ta Legas sun dora kasuwar baje kolin a ma’aunin kasuwa mafi girma a Najeriya, yammaci da tsakiyar Afirka da ake budewa.

Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya na shirye-shiryen bude kasuwar baje kolin wannan shekara wanda za a yi a karo na 35.

Za a bude kofofin kasuwar ne a Dandalin Tafawa Balewa na TBS da ke jihar daga ranar 5 zuwa 14 ga watan Nuwambar 2021.

Cibiyar kasuwancin jihar ta Legas ta ce ‘yan kasuwa kusan 1,500 daga kasashe 16 ne za su baje hajojinsu ga masu ziyara da aka yi kiyasin yawansu za su kai dubu 200,000.

Hukumomin jihar ta Legas sun dora kasuwar baje kolin a ma’aunin kasuwa mafi girma a Najeriya, yammaci da tsakiyar Afirka da ake budewa.

Daga cikin kayayyakin da za baje a kasuwar akwai kayayyakin da aka kera, masu ayyukan hannu da masu zane-zane, a wani mataki na bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Legas wacce ake mata taken “Cibiyar kasuwanci” ta kasance a sahun gaba wajen hada-hadar kasuwancin zamani a Najeriya da yammacin Afirka.

XS
SM
MD
LG