Kungiyar Likitocin Najeriya masu neman sanin makamar aiki ta NARD, ta sanar da janye yajin aikin da take yi.
Mambobin kungiyar sun kwashe sama da wata biyu suna yajin aiki saboda nuna korafinsu kan wasu bukatu da gwamnati ta gaza biya musu.
Rahotannin da dama daga Najeriya sun ruwaito shugaban NARD, Dr Dare Ishaya yana ba mambobin kungiyar umarnin su koma bakin aiki a ranar Laraba mai zuwa.
A ranar Litinin kungiyar ta janye yajin aikin bayan wani taro da ta yi a ranar Lahadi zuwa wayewar garin Litinin.
A cewar Dr. Ishaya, sun dauki matakin janye yajin aikin ne bayan kuri’a da suka kada wacce masu ra’ayin a koma bakin aiki suka samu dan karamin rinjaye kamar yadda Channels ya ruwaito.
Sai dai kungiyar ta ce ta janye ne iya tsawon mako shida don ta ba gwamnatin damar daukan matakan da za su biya musu bukatunsu.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kungiyar ta zabi komawa aiki ranar Laraba ne saboda ta ba mambobinta da suka yi tafiya dama su koma wuraren aikinsu.
A ranar 2 ga watan Agusta kungiyar ta shiga yajin aiki, inda ta nemi gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta da ta yi alkawari a baya ciki har da batun biyan kudaden alawus-alawus da suke bin gwamanati.