Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPC Ya Ci Ribar Naira Biliyan 287 – Buhari


Shugaba Buhari (Instagram/Muhammadu Buhari)
Shugaba Buhari (Instagram/Muhammadu Buhari)

Wannan shi ne karon farko cikin shekara 44 da kamfanin NNPC ya bayyana baki dayan ribar da ya samu tun da aka kafa shi in ji sanarwar Femi Adesina.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kamfanin man fetur din kasar na NNPC ya samu ribar naira biliyan 287 a shekarar 2020.

Wata sanarwa da kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana samun ribar ne bayan da aka kammala kididdige kudaden da kamfanin ya samu da wanda ya kashe a shekarar 2020.

“Ina mai farin cikin sanar da samun ribar naira biliyan 287 da NNPC ya yi a shekarar 2020.” Shugaba Buhari wanda har ila yau shi ne ministan man fetur din kasar ya ce cikin sanarwar.

Wannan shi ne karon farko cikin shekara 44 da kamfanin na NNPC ya bayyana baki dayan ribar da ya samu bayan da aka cire haraji in ji Adesina.

Shugaba NNPC Mele Kyari (Instagram/Mele Kyari)
Shugaba NNPC Mele Kyari (Instagram/Mele Kyari)

Wannan kuma a cewar Adesina, alkawari ne da gwamnatin tarayya ta yi a baya na cewa za ta rika bayyana halin da kamfanin yake ciki dangane da abin da ya shafi sha’anin kudade da ake sarrafawa.

A cewar sanarwar, “kamfanin na NNPC ya kuma rage yawan asarar da ya yi d aga naira biliyan 803 a 2018 zuwa naira biliyan 1.7 a 2019.

“Wannan abin alfahari, na daga cikin muradun wannan gwamnati na himmatuwa wajen tabbatar da ana tafiyar da kudaden jama’a da ake samu ta hanyoyin albarkatun kasar cikin hikima.”

Shugaban na Najeriya ya kuma ce, ya ba kamfanin na NNPC umarnin ya rika wallafa kudaden da ake sarrafawa na kamfanin akan lokaci, kamar yadda doka ta tanada “don a tabbatar da gaskiya bisa yadda ma’aikatun gwamnati” ke tafiyar da kudaden jama’a.

XS
SM
MD
LG