Kananan hukumomin da gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da rufe kasuwannin na mako-makon dai sune Birnin Gwari, Giwa, Kajuru, Igabi da kuma Chukun.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan wanda ya fitar da sanarwar ya ce gwamnatin ta haramta sayar da mai a jarkuna a wadannan kananan hukumomi biyar. "
"Bisa la’akari da halin da ake ciki da kuma yunkurin da jami’an tsaro da gwamnati suke yi na ganin cewa an fadada harkar tsaro, shi ya sa aka kafa dokar na dakatar da kasuwannin mako-mako a wadannan kananan hukukomi guda biyar" In ji Aruwan.
Tuni dai wasu 'yan-kasuwa su ka fara nuna damuwa game da wannan sabon mataki, Alhaji Shehu Mohammed Mai-gona Gulma, shi ne tsohon shugaban kungiyar kananan 'yan-kasuwa a Kawo a Kaduna kuma ya ce lallai yin hakan akwai damuwa.
"Gaskiya wannan sanarwar ba ta yi mana dadi ba kwata-kwata. Yanzu mutane suna cikin ha'ula'i, mutane suna tashi babu abinci babu kudin makaranta."
Masana harkokin tsaro dai a ganin matakin rufe kasuwannin ba zai magance matsalar tsaro a Arewa ba. Dakta Yahuza Ahmed Getso ya na cikin masu irin wannan ra'ayi.
"In ka hana zuwa kasuwa a jihar Kaduna da Zamfara, jihar Sokoto fa? wannan rufe kasuwa da ake magana, ba zai kai mu ko ina ba kuma ba mafita ba ne." A cewar Ahmed Getso.
Dama dai a makon jiya gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe wasu kasuwannin jim kadan bayan kai hari a makarantar horar da sojojin Najeriya ta NDA sai kuma gashi a wannan mako ta kara rufe kasuwanni bayan kisan gillan da aka yiwa Captain Abdulkareem Bala Ibn Na'Allah a Kaduna.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: