Kungiyar likitocin Najeriya ta kasa da ake kira NMA a takaice reshen babban birnin taraiyya Abuja ta koka a sakamakon rasa mambobinta 20 a makon da ya gabata a dalilin kamuwa da cutar coronavirus.
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya tace gwamnatin kasar na bukatar kudi kimanin nera biliyan 400 don kaddamar da allurar rigakafin cutar korona.
Likitoci a Kenya da ke aiki a asibitocin gwamnati sun fara yajin aikin gama gari ranar Litinin 21 ga watan Disamba akan rashin Insura mai kyau da kuma kayan kariya a yayin da su ke jinyar masu cutar COVID-19, a cewar kungiyar jami’an lafiyar.
Matakan bada tallafin sun hada da taimaka wa masana'antu don ma'aikatansu su ci gaba da aiki, da kuma ba Amurkawa tallafin kudi na kai tsaye.
Sama da mutane miliyan 75 suka kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya a cewar cibiyar da ke bin diddigin annobar coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins ranar Asabar 19 ga watan Disamba.
Kwanaki 5 bayan sace wasu daliban makarantar sakandare da ‘yan bindiga su ka yi a garin Kankara da ke jihar Katsina, wasu jihohin arewacin Najeriya sun dauki matakin rufe makarantunsu. Sai dai jama’a da sauran masana harkokin ilimi na ganin wannan tamkar bada kai ne ga ‘yan ta’adda a kasar.
Biyo bayan rasuwar wani babban Janar na rundunar sojan Najeriya da ya halarci wani taro, gwaji ya nuna an sami karin wasu manyan hafsoshin kasar da suka kamu da cutar COVID-19.
Kungiyar ‘yan jarida a Nijer ta koka a game da yadda anobar COVID-19 ta raba wasu ma’aikatan kafafen yada labarai masu zaman kansu da aiki sanadiyyar karancin kudaden shiga.
Shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta (WHO) ya ce an samu labaran kamuwa da COVID-19 a fadin duniya a cikin makwanni hudu fiye da watanni shidan farkon da annobar ta barke.
Birnin New York ya umarci makarantu su rufe ranar Laraba, yayin da garin ya sami karin yawan masu kamuwa da coronavirus kwanaki bakwai a jere sama da kashi uku cikin 100.
Amurka ta kara sumun adadin tarihi na masu kamuwa da coronavirus a rana guda.
Yayin da ake cigaba da bayyana farin cikin samun maganin corona mai ingancin kashi 90 cikin 100, kwararru sun ce a bi a hankali, kai a yi watsi da batun sanya takunkumin baki. Hangen Dala, ba shiga birni ba.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.