Taron shugabannin kungiyoyin ‘yan jaridar nahiyar Afrika da ya gudana a kasar Afrika ta kudu a watan Yunin shekarar 2007 ne ya bukaci shugabannin kasashe su rattaba hannu akan wani tsarin daftarin da ke hangen kawo karshen dabi’ar kulle ‘yan jarida a kurkuku saboda dalilai masu nasaba da aikin watsa labarai. A Nijer, a ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 ne Shugaba Issouhou Mahamadou ya saka hannu akan wannan takarda da ake kira 'declaration de la table de la montagne' da nufin sakarwa ‘yan jarida ragama.
A cewar shugaban cibiyar ‘yan jarida Ibrahim Harouna, daga wancan lokaci kawo yanzu an sami ci gaba a fannin ‘yancin aikin jarida, ko da ya ke wasu matsaloli sun gitta.
Domin karfafa wa ‘yan jarida gwiwa a irin wannan lokaci ya sa cibiyar Maison de la presse ta shirya wata gasa inda aka rarraba tukuici ga wadanda suka hada muhimman rahotanni masu la’akari da matsalolin jama’a. ‘Yar jarida daga tashar TV chanal 3, Rachida Ousmane na daga cikin wadanda suka sami irin wannan tukuici.
Ministan watsa labarai Habi Mahamadou Salissou, wanda ya jagoranci bukin karrama ranar ta 30 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da duba hanyoyin saka hannu akan wata yarjejeniya da ta yi tanadin albashi mai tsoka ga ma’aikatan watsa labarai. Ya kuma jan hankalin ‘yan jarida akan maganar adalci a tsakanin ‘yan takara a wannan lokaci da ake gab da soma yakin neman zabe.
Ga karin bayani cikin sauti: