Labarin nan mai nuna cewa an yi kusa a samu rigakafin cutar corona na kara kwarin gwiwar cewa an yi kusa aga bayan annobar COVID-19.
Kamfanin harhada magunguna na Pfizer da mai hada hannun da shi BioNTech sun sanar shekaran jiya Litini cewa ingancin rigakafin da su ka kirkiro ya ma zarce kashi 90% a wani bincike da aka yi.
Labaran ya zama mai matukar karfafa gwiwa, to amma kwararru sun yi gargadin cewa kar mutane su yar da kyallayen rufe fuskokinsu tukunna.
Kwararru sun ce ayi taka tsantsan saboda masu ilimin kimiyya na wasu wuraren ba su tantance bayanan ba tukunna. Su ka ce koda ma hakan ya tabbata, ba lallai ba ne rigakafin ya yi aiki da kyau kan sauran mutane kamar yadda ya y ikan mutanen da aka yi gwaji kansu.
To amma, a cewarsu, wannan sakamakon binciken mai karfafa gwiwa ne. Daraktan Cibayar Yaki Da Cututtuka Masu Yado Ta Amurka, Anthony Fauci, ya ce gano cewa rigakafin na da ingancin sama da kashi 90% wani babban abin mamaki ne.
Facebook Forum