A taron manema labarai da ya saba yi a helkwatan WHO a birnin Geneva, babban darektan hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fada a jiya Juma’a cewa asibitoci da sashen kulan gaggawa sun cika makil da jama’a a Turai da Amurka.
Sama da mutum miliyan 57 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin duniya tun da annobar ta barke kana sama da mutum miliyan daya da dubu dari uku ne suka mutu da cutar a cewar alkalummar cibiyar sa ido a kan cutar ta jami’ar John Hopkins.
An samu kmauwa da cutar mai yawan gaske a jiya Juma’a, inda a nahiyar Turai wadanda suka kamu suka haura miliyan 15, sama da mutum miliyan 9 ne kuma suka kamu a India kana dubu dari ne suka mutu da cutar. Kasar Mexico itace ta hudu da cutar tafi yawan illa, bayan Amurka da Brazil da kuma India, a cewar jami’ar John Hopkins.
Har iyau Amurka ke kan gaba a jerin kasashen da cutar COVID-19 tafi kama mutane, inda mutum miliyan 11 da dubu dari bakwai suka kamu da cutar, a cewar John Hopkins.
Amurka ta kiyasta a yanzu cewa sama da mutum dubu daya da dari uku (1,300) ke mutuwa da COVID-19 a duk rana, adadi mafi yawa tun lokacin da cutar ta yadu ta kuma yi tsanani a birnin New York.
Katafaren kamfanin harhada magunguna a nan Amurka Pfizer da BioNTech da suke aiki tare, sun fada a jiya Juma’a cewa sun shigar da bukatar gaggawa na neman izini daga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka domin a fara amfani da maganin su na rigakafi, suna fadin cewa a shriye suke su raba maganin sa’o’I kalilan da zarar an basu izinin.
Shigar da bukatar ya biyo bayan kalaman kamfanonin cewa gwajin maganin da suka gudanar ya nuna kaifin maganin ya yi kashi 95 cikin dari kana babu wata matsala da aka samu ya zuwa yanzu.
Sakataren kiwon lafiyar Amurka, Alex Azar, ya fada a jiya Juma’a akwai yiwuwar hukumar abinci da magunguna ta yanke hukunci a kan maganin a cikin ‘yan makwanni.