Biyo bayan rasuwar wani babban Janar na rundunar sojan Najeriya da ya halarci wani taro, gwaji ya nuna an sami karin wasu manyan hafsoshin kasar da suka kamu da cutar COVID-19.
Kungiyar ‘yan jarida a Nijer ta koka a game da yadda anobar COVID-19 ta raba wasu ma’aikatan kafafen yada labarai masu zaman kansu da aiki sanadiyyar karancin kudaden shiga.
Shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta (WHO) ya ce an samu labaran kamuwa da COVID-19 a fadin duniya a cikin makwanni hudu fiye da watanni shidan farkon da annobar ta barke.
Birnin New York ya umarci makarantu su rufe ranar Laraba, yayin da garin ya sami karin yawan masu kamuwa da coronavirus kwanaki bakwai a jere sama da kashi uku cikin 100.
Amurka ta kara sumun adadin tarihi na masu kamuwa da coronavirus a rana guda.
Yayin da ake cigaba da bayyana farin cikin samun maganin corona mai ingancin kashi 90 cikin 100, kwararru sun ce a bi a hankali, kai a yi watsi da batun sanya takunkumin baki. Hangen Dala, ba shiga birni ba.
Gwajin rigakafin cutar coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar, ya nuna sakamako mai kyau da ya wuce yadda aka yi tunanin samu a baya.
A jiya Litinin hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO ta sake yiwa kasashe kashedi cewa a daina saka siyasa a harkar annobar COVID-19, tana mai cewa yin haka na kawo rudani da rashin girmama masana kimiya kana cutar na kara ta’azzara.
Kasar Kenya na fuskantar barazanar zagaye na biyu na yaduwar cutar coronavirus inda alkalumar wadanda ke dauke da cutar ke kara hauhawa.
Da alamar dai hauhawar annobar COVID-19 da aka yi hasashen zai fara yayin da yanayin sanyi ke karatowa a bangaren duniya da ke arewa da kuryar equator, yana kan faruwa.
Uwargidan shugaban Amurka Melania Trump tace danta Barron Trump mai shekaru 14 da haifuwa ya kamu da coronavirus amma tuni gwaji ya tabbatar ya warke, bashi dauke da kwayar cutar kuma.
Hukumar Lafiya Ta Duniya, wato WHO, ta ce mai yiwuwa matasa da mutane masu lafiya za su jira zuwa shekarar 2022 kafin ayi musu allurar rigakafin COVID-19. Dalilin haka shi ne aga cewa allurar ta wadaci masu tsananin bukatarta.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.