'Yan kasar Nijar sun yi kira ga al'umomin Najeriya da 'yan siyasa su kaucewa duk wasu hanyoyi da zasu haddasa tashin hankali a kasar lokacin zabe.
Jam’iyyar PRP a jihar Bauchi ta zargi hukumar yan sandan jihar da da kame magoya bayanta guda 22.
Amurka ta jaddada bukatar dake akwai na gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a Najeriya.
Dan takarar gwamnan jihar Plato karkashin tutar jam’iyar PDP Saneta Jeremiah Useni ya bayyana cewa, duk da yake burin matasa da dama na tsayawa takara a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara bai cika ba, suna da rawar da zasu taka a harkokin mulki.
Uwargidan dan takarar shugaban kasa a Najeriya na jam’iyar DPD Hajiya Amina Titi Atiku Abubakar ta yi kira ga matasa su guji bangar siyasa a lokutan zabe.
Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta kama wasu matasa da ba ta bayyana yawan su ba, dauke da wasu buhuna guda 17 makare da takardun kuri'ar zabe wato Ballot paper da ake zargin cewa, za a yi safarar su zuwa jihar Jigawa.
Ya yin da shirye-shiryen zabe ya kankama a Najeriya, masu sharshi a jamhuriyar Nijar sun fara bayyana matsayinsu a game faruwar wasu abubuwan da ke nuna alamun Nijar na goyon bayan daya daga cikin ‘yan takarar zaben shugaban kasa mai zuwa.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna, ta koka da kama wasu manyan jam'iyyar da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi saboda wasu kalamai da suka yi da ake zargin za su iya ta da fitina a ranar zabe.
Yayin da zaben najeriya ya rage kwanaki uku, yanzu haka ana samu karin kalaman batanci daga bakin 'yan siyasa wanda ka iya tunzura magoya bayansu wajan aikata ba daidai ba, musamman a tsakanin jam'iyyun APC da PDP.
Domin Kari