Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar da jawabin karshe gabanin gudanar da zaben nan a ranar Asabar din nan.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a tabbatar da tsaro a rumfunan zabe gobe Asabar a lokacin da za a gudanar da babban zabe a kasar, mako daya bayan da aka dage zaben.
Shugaban ‘yan sandan Najeriya ya aikewa masu shirin tayar da fituna gargadin karshe a zaben shugaban kasar da za a gudanar gobe Asabar a Najeriya.
Hadakar kungiyoyi a jihar Taraba ta koka da tura karin sojoji a jihar, saboda fargabar da mutane suka shiga a shirye shiryen zaben da za a yi gobe.
A yayinda ya rage kasa da sao'i 48 a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, shugabannin al’umma a yankin kudancin Najeriya na ci gaba da kira ga 'yan kasa musanmman matasa dasu fito domin kada kuri’unsu domin samun nasarar zaben.
Yayin da Najeriya ke fuskantar zabe a ranar Asabar mai zuwa, rundunar soji ta shida da ke Fatakol a jihar Rivers, sun gano ana shirin yin amfani da wasu bata gari domin ta da hankalin masu jefa kuri'a ranar zabe.
Tshohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa da za'a yi ranar Asabar mai zuwa.
Ra'ayin Abdulrazak Sulaiman Daga Jos Akan Babban Zaben 2019. Mene'ne ra'ayinku akan wannan lamari?
Ra'ayin Patricia Onoja Daga Abuja Akan Babban Zaben 2019. Mene'ne ra'ayinku akan wannan lamari?
Domin Kari