Shugaban dai wanda ya godewa magoya bayan sa, ya kuma yi sauri ya bukaci gujewa murnar da ta wuce kima ko habaici ga abokan hamaiya.
Hakanan ya zaiyana zaben a matsayin wanda a ka yi gudanar cikin adalci, inda ya ba da tabbacin ci gaba da aikin yaki da cin hanci da sauran alkawuran kamfen.
Shugabannin APC, ‘yan majalisar dokokin tarayya da manyan magoya baya su ka rufawa shugaban baya a taron.
Sakataren APC Mai Mala Mala Buni ya zaiyana lashe zaben a matsayin gagarumar nasara ga masu son sauya akalar mulki daga ‘yan jari hujja zuwa talakawa.
Jim kadan bayan kammala wannan taro ita ma PDP ta gudanar da taro inda ta yi watsi da sakamakon zaben.
Nan ma dan takarar PDP Atiku Abubakar ke kin amincewa da sakamakon da zaiyana cewa ko a gwamnatin soja ba a taba gudanar da zabe marar kan gado irin wannan ba.
Atiku ya yi ikirarin cewa daga sanar da sakamakon, Najeriya ta yi asarar Naira biliyan 85 daga masu zuba jari.
Jam’iyyar PDP ta ce za ta sanar da matakan da za ta dauka a gaba da kira ga magoya bayan ta su kwantar da hankalain su.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum