Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijer Mahammadu Isuhu Ya Taya Shugaba Buhari Murna


Shugaban kasar Nijer  ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari sakon taya murna sakamakon lashe  zaben da akayi a kasar. Mahamadu Isuhu ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata dama da za ta baiwa gwamnatocin kasashen 2 sukunin ci gaba da aiyukan hadin guiwa tsakaninsu.

Shugaban Nijer dake cikin na farko farko a jerin shuwagabanin kasashen da suka aikewa shugaba Buhari sakon taya murnar galabar da ya samu a zaben asabar din da ta shige ya rubuta a shafinsa na twitter cewa ina farin ciki da hukumomin kula da harakar zaben Najeriya suka bayyana sakamakon zaben da ya gudana a ranar 23 ga watan fabreru wanda ya baiwa shugaba Buhari nasarar lashe zabe a karo na biyu don ganin ya ci gaba da shugabancin Najeriya abin da a fili yake nunin an samu ci gaban dimokradiya a wannan yankin.

Issoufou Mahamadou, a ci gaban wannan wasika da a dai gefe aka gabatar da ita a kafafen mallakar gwamnatin NIjer ya jinjinawa al’umar Najeriya saboda halin dattakon da yace sun nuna a yayin wannan zabe sannan ya yabawa hukumar zaben kasar wace yace cikin kwarewa ta tafiyarda tsare tsaren zaben da masu sa ido suka kira sahihi wanda ya gudana cikin yanayin haske da adalci.

Shugaban yace al’umar Nijer na mai alfahari da nasarar ta Mahammadu Buhari saboda a cewarsa al’amari ne da ke kara karfafa aiyukan hadin guiwar da kasashen biyu suka sa gaba wadanda ke hangen kara dankon zumunci da karfafa zaman lafiya da tsaro a baki dayan wannan yanki.

A karshe shugaba Issouhou ya kara jaddadawa shugaba Buhari cewa a shirye yake su ci gaba da aiki tare domin tunkarar dukkan wani kalubalen dake gaban Nijer da Najeriya da ma baki dayan yankin Afirka ta yamma.

Da ma dai tun a yayin yakin zaben kasar ta Najeriya alamomi ke nuna cewa ra’ayin mahukuntan Nijer ya fi karkata ga dan takarar APC Muhammadu Buhari bayan da aka hango gwamnan Maradi da na Zinder a wurin gangamin da jam’iyar mai mulkin Najeriya ta gudanar a Kano kafin daga bisani a soma jin wata wakar da kungiyar Albishir ta Nijer ta rera wa dan takara Buhari da nufin farfagandan zabe.

A shekarar 2015 Jamhuriyar Nijer ce kasar da Mahamadu Buhari ya zaba don kaddamar da ziyarce ziayrcensa zuwa waje a matsayinsa na shugaban tarayyar Najeriya lamarin da ake alakantawa da 'yan uwantakar dake tsakanin wadanan kasashen biyu .

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG