Alkali Ruth Ginsburg wadda ta dade a matsayin alkalin kotun Amurka ta rasu yau jumma'a bayan ta yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Ma’aikatar harkokin kasuwancin Amurka ta ce za ta fitar da wani umurni a ranar Juma’a wanda zai hana jama’ar kasar sauke manhajojin WeChat da TikTok na kasar China.
Bayanan binciken sirri na nuni da cewa har yanzu Rasha na kokarin yin kutse da katsalandan domin sauya sakamakon zaben Amurka na shekara ta 2020, kamar yadda ta yi a zaben shekara ta 2016.
Sanadiyyar Dirowa da mahaukaciyar guguwar nan ta Sally ta yi a yankunan gabar teku musamman a jahar Alabama ta Amurka, mutane da dama sun rasa wutar lantarki baya ga wasu nau'ukan barna masu yawan gaske.
Kamar yadda tsirarun jinsi su ka fi Turawa kamuwa da cutar a Amurka a bangaren manya, a bangaren matasa ma haka abin ya ke, tsirarun jinsi sun fi kamuwa.
Akwai alamar mahaukaciyar guguwar nan ta Sally za ta janyo ambaliyar ruwa idan ta karasa dannowa zuwa gabar teku a yau Laraba a Amurka.
Jiya Talata shugaban shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranci bukin rattaba hannu a fadar White House, na yarjejeniyar maido da hulda tsakanin kasar Isira’ila da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.
Gwamnatin Amurka ta dauki matakin tsabtace tsarin zaben Najeriya ta hanyar da zata shafi manyan ‘yan siyasa masu ikon fada a ji.
A wani al'amari mai cike da tarihi, wasu kasashen Larabawa biyu, wato da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, za su rattaba hannu kan yarjajjeniyar hulda da kasar Isira'ila.
Shugaba Donald Trump da abokin karawarsa na jami’iyar Democrat Joe Biden sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi a jiya Litinin a kan abin da ya tada gobarar daji mai tarihi da ta yi barna a yammacin Amurka da ta kasheakalla mutum 35.
Domin Kari