A yau Talata aka yi bikin bude sabuwar cibiyar ma’aikatar shige da fice a Jamhuriyar Nijer, wadda gwamnatin Amurka ta dauki dawainiyar ginawa a ci gaba da karfafa matakan dakile hanyoyin da masu miyagun ayyuka ke amfani da su wajen ta’asar dake da nasaba da ta’addanci.
Yanayin da ake ciki a yankin sahel wani abu ne dake bukatar zuba ido sosai akan sha’anin kai da kamon jama’a musamman a iyakokin kasashen dake fama da ayyukan ta’addanci, safarar bil adama, miyagun kwayoyi da makamai, wadannan na daga cikin dalilan da yasa gwamnatin Amurka ta dauki nauyin gina wa kasar Nijer sabuwar ma’aikatar shige da fice DST mai dauke da kayan aiki na zamani, domin tunkarar wannan kalubale inji jakadan Amurka a Nijer, Eric Whitaker.
Ministan harkokin cikin gidan Nijer Alkache Alhada ya ce, ayyukan binciken baki ‘yan kasar waje akan iyakoki da sanya ido akan maganar kwararar bakin haure da ayyukan masu ketarar da ‘yan cirani da safarar bil adama na daga cikin ayyukan da sabuwar ma’aikatar za ta maida hankali akansu. Sannan kuma ke da alhakin buga fasfo da dukkan wasu takardun.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda kuma darektan sashen kula da hulda da jama’a, Commissaire Abou Mountari ya jinjina wa gwamnatin Amurka da sauran abokan hulda saboda gudunmawar da suka bayar wajen ganin an gina sabuwar ma’aikatar ta DST. kimanin million 1700 na cfa, Amurka ta kashe wajen gudanar da wannan aiki.
Saurari cikakken rahoton Sule Barma cikin sauti:
Facebook Forum