Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Karbi Bakuncin Bukin Rattaba Hannu Tsakanin Isira'ila da Wasu Kasashen Larabawa Biyu


Tutocin Hadaddiyar Daular Larabawa, Isira'ila da Bahrain
Tutocin Hadaddiyar Daular Larabawa, Isira'ila da Bahrain

A wani al'amari mai cike da tarihi, wasu kasashen Larabawa biyu, wato da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, za su rattaba hannu kan yarjajjeniyar hulda da kasar Isira'ila.

Shugaban Amurka Donald Trump zai karbi bakuncin bukin rattaba hannu a fadar White House a yau dinnan Talata, na yarjejeniyar maido da hulda tsakanin kasar Isira’ila da wasu kasashen Larabawa: wato Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.

Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Abdullah bin Zayed, za su rattaba hannu kan yarjejeniyar da ake wa lakabi da “Abraham Accord”, ma’ana yarjajjeniyar girmama Annabi Ibrahim, uban Yahudu da Labara, a shiyyar kudu ta fadar White House.

An fara cimma yarjajjeniya tsakanin Isira’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa ne ran 13 ga watan Agusta; sai kuma ranar Jumma’a da ta gabata, ita ma kasar Bahrain ta ce za ta kulla dangantaka da kasar ta Yahudu.

A karkashin wannan yarjajjeniyar ta Abraham Accords, Firaminista Netanyahu ya amince ya tsai da shirin hade sassan Yammacin Kogin Jordan. Masu lura da al’amura na ganin wannan wata alama ce ta canjin tunani a Gabas Ta Tsakiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG