Wani sabon rahoto ya nuna cewa annobar COVID-19 ta janyo tafiyar hawainiya, a ci gaban da aka samu wajen rage talauci da rashin koshin lafiya a duniya.
Rahoton shekara shekara mai suna "Goalkeepers Report", na gidauniyar Bill and Melinda Gate, wadda hamshakin attajirin nan mai kamfanin Microsoft da matarsa su ka kirkiro don ayyukan taimako, ya gano cewa mutane kusan miliyan 37 sun fada cikin matukar talauci tun daga farkon aukuwar annobar, kuma yawansu ya yi ta karuwa da kashi 7% cikin ‘yan watanni kalilan kawai.
A halin da ake ciki kuma, kason yaran da ke samun rigakafi na yau da kullum, na cututtuka irinsu bakon dauro da sauransu, ya ragu daga 80% na bara zuwa kashi 70% a wannan shekara ta 2020, wanda rahoton ya ce rabon a ga haka tun wajejen shekarar 1990.
“Mun koma baya da shekaru wajen 25 cikin wajen makonni 25 kawai,” a cewar rahoton, wanda ke bibiyar ci gaba mai dorewa a muradun Majalisar Dinkin Duniya.
Facebook Forum