A jiya Alhamis daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka - FBI, Christopher Wray, ya fadawa ‘yan majalisar dokoki cewa, Rasha ba ta ja da baya ba a kokarin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.
Wannan ya tabbatar da bayanan da hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta bayar a can baya cewa, babbar manufar Moscow shi ne ta lalata gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.
Da yake ba da bahasi a gaban kwamitin tsaron cikin gida na majalisar, Wray ya kwatanta tasirin aikin Kremlin da cewa mai karfin gaske ne a kan shafukan sada zumunta da kafar yada labaranta da ma wasu hanyoyi da dama.
"Babban abin da Rasha take so ta cimma shine durkusar da mataimakin shugaban kasa Biden da kuma abin da Rasha din ke kallo a matsayin kin jininta," inji Wray.
Kalaman na daraktan hukumar ta FBI sun yi daidai da hasashen jama’a a farkon watan Agusta da ba a saba gani ba, game da barazanar da zaben Amurka ke fuskanta da babban jami’in hukumar leken asirin Amurka William Evanina ya bayyana.
Facebook Forum