Fafatawar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da tsohon shugaban kasa Donald Trump yau Talata 10 ga watan Satumba da karfe 9 na dare agogon ET da Laraba 11 ga watan Satumban da muke ciki da na safe 1 dare agogon UTC.
Kiyasi ya nuna mutum miliyan 51.3 ne suka kalli muhawarar Trump da Biden a watan Yuni, ana kuma hasashen wadanda za su kalli ta Trump da Harris za su haura wannan adadi.
Trump da Harris za su kwashe tsawon mintuna 90 suna mayar da juna martani, yayin da suke amsa tambayoyi da masu gabatar da labarai a tashar ABC NEWS, David Muir da Linsey Davis za su yi musu.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce mutane 55 ne suka mutu yayin da wasu 328 suka jikkata a a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Poltava, kan wata cibiyar horar da sojoji da kuma wani asibiti da ke kusa.
Sanarwar ta ma'aikatar lafiya ta kasar ta kara da cewa, "sakamakon hare-haren na Isra'ila, an kashe ma'aikatan jinya 25 daga tawagar motocin daukar marasa lafiya daban-daban, tare da ma'aikatan lafiya biyu, sannan ma'aikatan jinya da ma'aikatan lafiya 94 sun jikkata."
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito wasu jami’ai da ba’a bayyana sunayensu ba, suna tabbatar da cewa a ‘yan kwanakin nan Iran ta ba da makamai masu linzami ga Rasha, a karkashin wani shiri da zai zama na farko na habakar kawancen soji tsakanin kawayen kasashen 2 masu adawa da yammaci.
Wadanda suka zambatar sun hada da wani matashi dan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kan sa da kan sa.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa bude wutar da aka yi a wata babbar sakandare a jihar Georgia ta Amurka a jiya Laraba, ya hallaka akalla mutane 4 tare da raunata wasu 9.
Tsohon shugaba Trump, kuma dan takarar jami’iyar Republican a zaben 5 ga watan Nuwamban 2024, ya ajiye damarsa ta bayyana a gaban kotu, kana maimakon haka ya umarci lauyoyin sa su shigar da karar a madadin sa.
Shagunan sayar da kayyaki kan yi amfani da wannan lokacin biki wajen karya farashin kayayyaki a sassan kasar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce jami'ansa sun tuntubi Isra'ila wadda ta tabbatar da gano gawarwakin a Gaza. Biden ba shi da tabbacin adadin gawarwakin. Ya kuma kara da cewa ba shi da 'yancin tantance gawarwakin a halin yanzu.
Gwamnatin Taliban ta Afghanistan da ke ganin jiragen na kasar ta Afganistan ne, sun ki amincewa da mika su ga Uzbekistan.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.