Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris, Trump Za Su Fafata A Muhawara Mai Zafi A Daren Talata


Mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da tsohon shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican
Mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da tsohon shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican

Trump da Harris za su kwashe tsawon mintuna 90 suna mayar da juna martani, yayin da suke amsa tambayoyi da masu gabatar da labarai a tashar ABC NEWS, David Muir da Linsey Davis za su yi musu.

An shirya tsaf don gudanar da muhawarar da za’a yi a daren ranar Talata tsakanin mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da kuma tsohon shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican, wani mataki a mai muhimmanci a yakin neman zaben shugaban Amurka da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba.

‘Yan takarar biyu ba su taba haduwa da juna ba ko ma yin magana ta wayar tarho, amma a ranar Talata za su tsaya nesa kadan da juna a bayan munbari a Cibiyar Tsarin Mulki ta Kasa da ke Philadelphia a jihar Pennsylvania.

Trump da Harris za su kwashe tsawon mintuna 90 suna mayar wa da juna martani, yayin da suke amsa tambayoyi da masu gabatar da labarai a tashar ABC NEWS, David Muir da Linsey Davis za su yi musu.

Miliyoyin Amurkawa ne ake hasashen za su kalli karawar tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa za su yi a wata muhawara ta yakin neman zabe. Ana gudanar da muhawarar ne makonni takwas kafin ranar zabe a hukumance, amma kwanakin kadan kafin fara kada kuri’a da wuri a wasu jihohi 50 na kasar.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta kasa ta nuna cewa zaben babu tazara tsakaninsu, wanda hakan ya sanya dukkan ‘yan takarar biyu za su iya yin amfani da damarsu a muhawar ga ‘yan tsirarun masu kada kuri’a wadanda ba su riga sun yanke shawarar wanda za su zaba ba.

Abin da ke a kasa, komawar Trump fadar White House bayan da ya sha kaye a zaben 2020 ga hannun shugaba Joe Biden ko kuma ya daukaka Harris, mataimakiyar Biden.

Lokacin da Biden ya fice daga sake neman takara a watan Yuli bayan rashin tabuka komai a muhawara da Trump a karshen watan Yuni kuma ya goyi bayan Harris a matsayin wacce za ta gaje shi, ‘yan Democrat sun hada kai na goyon bayan takararta.

Yayin da Biden ya kasance yana biye da Trump lokacin da ya kawo karshen yakin neman zaben sa, Harris ta wuce Trump a kuri’ar jin ra’ayin jama’a na kasa da dama da maki biyu ko uku cikin 100.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da jaridar New York Time da Kwalejin Siena suka fitar a ranar Lahadi ta nuna cewa Trump yana da kashi 48 zuwa 47 cikin 100 da yake kan gaba a kasa bakin daya kamar yadda jaridar ta nuna Harris a gaba a matsakaicin kuri’ar jin ra’ayin jama’a da yawa a jihohi uku da za’a fafata sosai, Wisconsin, Michigan da Pennsylvania, tare da ‘yan takarar biyu sun yi kunnen doki a jihohi hudu masu muhimmanci, Nevada, Georgia, Arizona da kuma North

Ana sa ran za’a fafata sosai a jihohi bakwai da za su taka rawa wajen tantance sakamakon zaben saboda Amurka ba ta zabar shugaban kasa da mataimakinsa ta hanyar yawan kuri’un da aka zabe su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG