Shugaban Amurka Joe Biden ya ce jami'ansa sun tuntubi Isra'ila wadda ta tabbatar da gano gawarwakin a Gaza. Biden ba shi da tabbacin adadin gawarwakin. Ya kuma kara da cewa ba shi da 'yancin tantance gawarwakin a halin yanzu.
Gwamnatin Taliban ta Afghanistan da ke ganin jiragen na kasar ta Afganistan ne, sun ki amincewa da mika su ga Uzbekistan.
Sabuwar tuhumar ta cire batun zargin tattaunawa da aka ce Trump ya yi da Ma’aikatar Shari’a.
Wannan shi ne karo na farko da Harris za ta zanta da wata kafar yada labarai tun bayan da ta maye gurbin Shugaba Joe Biden wanda ya janye takararsa.
Wan Mai Shari’a A Amurka Ya Dakatar Da Shirin Da Ke Baiwa Iyalan Amurkawa Iziznin Zama 'yan Kasa
Tallan yunkuri ne na jan hankalin masu kada kuri’a a jihohin da ke da muhimmanci wajen samun kuri’u wadanda suka hada da Arizona da Nevada.
Gabbard ita ce ‘yar majalisar daya tilo da ta ki kada kuri’a a lokacin da majalisar wakilai ta tsige Trump saboda wasu huldodi da ya yi da Ukraine.
Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris ta ce yakin neman zabenta ya tara dala miliyan 540 ya zuwa yanzu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala harris, ta yi kira ga Amurkawa da su hada kai da a ranar Alhamis, yayin da take amincewa da zabenta da aka yi a matsayin ‘yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democrat.
Kusoshin jam'iyyar Democrat da dama sun yi jawabai a rana ta uku a babban taron kasa na jam'iyyarsu wanda ke gudana a birnin Chicago na jahar Illinois ta Amurka
A daren jiya an shiga babi na farko na daya daga cikin rukunoni mafiya muhimmanci na wannan taron, wato kiran ‘yan deliget daga jihohin Amurka, su yi shelar kada kuri’unsu ga ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta Democrat, Mataimakiyar Shugaban kasa, Kamala Harris.
Barack Obama ya gabatar da jawabi mai karfafa zuciya da kyakyawar fata akan takarar mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.