An harbe wani yaro dan shekara biyar kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti," a cewar shugaban 'yan sandan birnin Houstan, yayin da wani mutum ke jinyar harbin bindiga a kafa.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da bukatar kungiyar Hamas na tsagaita wuta tare da ba da umarni ga sojojin kasar da su shirya kutsawa birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Saudiyya a yau Litinin a ziyararsa ta biyar a yankin tun bayan barkewar yaki a yankin Gaza, yana fatan ci gaba da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma shiri bayan yakin da dakile tashe-tashen hankula a yankin.
Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya ta FIFA, ta sanar ranar Lahadi cewa za a buga wasan karshe na cin kofin duniya na shekarar 2026 a filin wasan Metlife da ke birnin New Jersey.
Amurka ta sake nanata kudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziki da kasuwanci a kasashen Afirka.
Wani mutum da ake zargi da fille kan mahaifinsa a birnin Philadelphia, ya wallafa wani bidiyon mai ban tsoro a shafukan sada zumunta wanda ya nuna shi yana rike da kan da ya yanke yana kuma zagin gwamnati, kamar yadda hukumomi suka fada jiya Laraba.
An cafke wani mutum da ake nema kan laifin kashe budurwarsa tare da barin gawarta a wani wurin ajiye motoci a filin jirgin sama na Boston kafin ya tashi zuwa Kenya, kamar yadda ‘yan sandan Kenya suka bayyana a jiya Talata.
Manyan kasashe masu ba da agaji da dama sun ce za su dakatar da bayar da kudade ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi na cewa ma'aikatanta na da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A ranar Laraba, wasu tankokin yaki guda biyu sun kai hari a matsugunin Majalisar Dinkin Duniya a Khan Yunis inda dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suka fake.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya hallarci wani taro da bankin raya Afurka ya shirya a birni Legas na samar da abinci da kuma tallafa wa manoman nahiyar.
Dexter Scott King, wanda ya sadaukar da yawancin rayuwarsa kan abin da ya gada daga iyayensa Rev. Martin Luther King Jr. da Coretta Scott King na fafutukar kare hakkin dan adam, ya rasu a ranar Litinin bayan ya yi fama da cutar sankara ta prostate. Ya rasu yana da shekaru 62.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.