Trump ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa cewa, "Ina farin cikin sanar da cewa Kari Lake ce za ta zamo daraktar Muryar Amurka mai zuwa,” ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Ms. Lake, tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye a kafar yada labarai ta Phoenix, a cewar Trump, za ta yi aiki tare da wanda zai jagoranci kafar yada labaran Amurka da ake sauraro a duk duniya wanda nan ba da jimawa ba, za’a bayyana sunansa domin tabbatar da cewar an yada muradan Amurka, ciki har da na fadin albarkacin baki yadda ya kamata.
Ms Lake ta yi martani da cewa “karramawa ce da Shugaba Trump ya bukace ne in jagorancin Murya Amurka.”
Ta kara da cewa, Muryar Amurka wata kafar yada labaran kasa da kasa ce mai muhimmancin gaske da aka kafa domin yada manufofin Amurka ta hanyar tattaunawa kai tsaye da al’ummomin duniya, tare da dabbaka akidun dimokiradiya, da gaskiya, ga masu sauraron da yawansu ya kai mutane miliyan 354.
Ta ci gaba da cewa, "Muryar Amurka na yada labarai cikin harsuna 49. A karkashin jagoranci na, Muryar Amurka za ta yi zarra kan manufarta, ta yada nasarorin Amurka a fadin duniya.”
Dandalin Mu Tattauna