Shekaru biyu bayan da mayakan boko haram suka sace dalibai, ‘yan mata sama da 200 a Arewacin Najeriya, wani sabon bidiyo ya nuna ‘yan matan watannin 4 da suka wuce ya sa iyaye sa ran daliban nan da rai.
A yayin da ake tuna cikar shekaru biyu da sace dalibai mata daga makarantar sakandare ta Chibok a Jihar Borno, an gudanar da gangami zuwa fadar shugaban Najeriya, Aso Villa, a Abuja.
Kamar sauran jihohi a Najeriya da sauran kasashen duniya, an gudanar da gangamin tunawa da sace yan matan Sakandaren Chibok da suka cika shekaru biyu a hannun yan kungiyar Boko Haram.
Jiya a garin Bauchi aka yi bikin cika shekaru hamsin da biyu da kafa rundunar sojin saman Najeriya inda hafsan hafsoshin sojojin kasar ya wakilci shugaban kasa Muhammad Buhari wanda kuma shi ne babban kwamandan duk sojojin Najeriya na kasa da na ruwa da na sama
Tun lokacin da gwamnatin Buhari ta kama mulki ta yi alkawarin ceto 'yan matan Chibok din nan da kungiyar Boko Haram ta sacesu daga makarantarsu yayinda suke rubuta jarabawar kammala karatun sakandare
Ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga makarantar sakandare ta 'yan mata dake garin Chibok suka sace 'yan makarantar su fiye da dari biyu kuma har yau ba' ji duriyarsu ba ko a san inda suke.
Kusan shekaru biyu kennan da aka sace ‘yan makarantar mata ta garin Chibok, har yanzu babu labarin su
Mayakan Boko Haram da ke Najeriya na dada amfani da yara kanana wajen kai hare-haren kunar bakin wake, a cewar Asusun Yara na majalisar dinkin duniya.
Domin Kari