Farfesa Wole Shoyinka ya kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen ganin an sako ‘yan matan Chibok fiye da 200 da ake garkuwa da su a wajen wani gangami da aka shirya domin tunawa ‘yan matan a jihar Lagos.
A bana kungiyoyin kare hakkin bil Adama da kuma hukumomi daban daban a ciki da wajen Najeriya, sun gudanar da irin wannan gangami na ganin an sako ‘yan matan. A birinin Lagos wata kungiya ta matasan jihohin yammacin Najeriya, sunyi kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen ganin an nemo ‘yan matan.
Mista Damilola Ajayi na daya daga cikin shugabannin wannan kungiya tace, “ko kadan bamu damu ba wayannan yan uwanmune da aka sace, ban damu ko Bahaushiya bace ko Beyerabiya a’a ‘yan Najeriya ne kuma ‘yan uwanmu, idan muka zauna mukayi shiru to abinda ke faruwa zai iya faruwama a wannan yankin.”
Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.