A firar da ya yi da Muryar Amurka mataimakin shugabn kasa na musamman akan harkokin labarai Garba Shehu ya bayyana abun da gwamnatin ta Buhari ke shirin yi akan 'yan matan Chibok da yau suka cika shekaru biyu a hannun 'yan Boko Haram da suka sacesu daga makarantarsu.
Lokacin da gwamnatin Buhari ta karbi mulki Garba Shehu yace akwai rahoto akan 'yan matan da ta gada da aka rubuta bisa ga binciken tsohuwar gwamnatin. To saidai da alama cewa an rubuta rahoton ne domin a wanke kowa da kowa.
Garba Shehu yace amma 'yan matan sun bata kuma babu yadda za'a e kowa ya yi aikinsa yadda ya kamata. Dalili ke nan da wannan gwamnatin tace zata yi bincike.
Saidai kuma lokacin da Shugaba Buhari ya sadu da wasu daga cikin iyayen yaran akwai wadanda suka ce sun san wani abun da gwamnati bata sani ba. Wasu kuma cewa suka yi hada baki aka yi. Tunda magana ta zama haka kamata ya yi a bincika a saurari kowa.
Shugaba Muhammad Buhari ya amince a kafa kwamitin bincike. An gabatar da sunayen wadanda zasu yi aikin kuma ya amince saboda aiki ne dake bukatar mutane kwararru da aka kuma amince dasu..
Akwai wasu da mai ba shugaban kasa a harkokin tsaro yake son ya yi anfani dasu a kwamitin amma an basu wani aiki suna yi sai sun kammala.
Ga karin bayani.