A cikin jawabin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yiwa taron bikin ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa wajen yakar 'yan ta'ada ta bakin babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Olorunnishakin wanda ya wakilceshi.
Shugaba Muhammad Buhari yace yana da masaniya cewa bikin yana da tasiri musamman ga sojojin da suka yi ritaya. Sabili da haka shugaban yace yanzu kasar take bukatar gudummawarsu musamman a yaki da masu tada kayar baya da kuma 'yan ta'ada.
Shi ma yayinda ya gana da manema labarai shugaban sojin saman Najeriya Air Marshall Sadiq Abubakar ya bayyana irin nasarorin da sojin saman Najeriya suka samu a cikin shekaru hamsin da biyu da kafuwa. Yace kafa sojin sama bai fi shekaru hudu ba da aka fara yakin basasa. Duk da cewa ba'a dade da kafata ba rundunar ta taka rawar gani a yakin.
Sojin saman Najeriya sun je kasashen Liberiya da Saliyau lokacin da suke yaki. Aikin yanzu ya fi na shekarun baya. Yace lokacin da aka yi yakin basasa ana mirgina bam da hannu ne. Amma yau rundunar tana da jiragen da batin kawai mayaki zai danna ya sakar da bam.
Dangane da dajin Sambisa Air Marshall Sadiq Abubakar yace saura lokaci kadan ne su gama da wurin.
Akan 'yan matan Chibok yace suna kai kuma ba kubutar da 'yan Chibok kawai suka sa gaba ba duk wadanda aka sace burinsu ne su kubutar dasu. Yace suna shawagi dare da rana su gano inda suke.
Dajin Sambisa babban waje ne. .
Ga karin bayani