Mr. Emmanuel Bello tsohon kwamishanan yada labarai wanda yake kan gaban a dawo da Gwamnan Danbaba Suntai yace ya samu sauki kuma kwanan nan zai koma bakin aikinsa.
Majalisardokokin jihar Taraba zata yi anfani da sashen kundun tsarin milkin da ya bata damar ta binciki lafiyar jikin gwamna Danbaba Suntai wanda yanzu ya kwashe watanni 22 yana jinya sanadiyar raunin da ya samu a hatsarin jirgin sama.
Hukumomi a jihar Taraba sun tabbatar da kashe mutane fiye da goma a Ibi tare da sace wasu 'yansanda biyu da mata da yara da jirgin ruwan kwale-kwale da suke ciki
Yayin da zaben shekarar 2015 ke karatowa siyasar jihar Taraba ta soma daukan wani salo inda wasu shugabannin kananan hukumomi ke fuskantar barazar tsigesu daga kujerunsu.
Siyasar jihar Taraba na neman sanya salo inda wasu dattawan jihar ke bukatar a tabbatar da mukaddashin gwamnan a matsayin gwamnan jihar
Jam’iyyar PDP a jihar Taraba ta gudanar da zaben fidda gwani domin cike gurbi na mazabar Takum, a majalisar dokokin jihar, na kujerar marigayi tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Honorable Haruna Tsokuwa.
Har yanzu ana kai ruwa rana tsakanin magoya bayan gwamna Suntai da magoya bayan mukaddashinsa yayin da yanzu ana zargin mukaddashin da musgunawa mutane
Tun da gwamna Danbaba Suntai ya dawo daga jinya babu wanda ya ganshi a bainar jama'a ko kuma ya jishi yana magana amma lamari ya canza domin gwamnan ya fitar da wani bidiyo inda ya fada karar cewa baya cikin koshin lafiya kuma ba zai iya komawa bakin aikinsa ba yanzu.
Yanzu haka a jihar Taraba an fara musayar kalamai tsakanin mukarraban gwmanan jihar Danbaba Suntai, da kuma bangaren mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar.
Dambarwar siyasa a jihar Taraba sai sake salo ta keyi inda yanzu wasu na hannun daman gwamna Danbaba Suntai suna zargin mukaddashinsa da yi masa daurin talala
Bayan rasuwar kakakin majalisar dokokin jihar Taraba makon jiya yanzu ta samu sabo
Wasu 'yanbindiga sun yi rashin sa'ar samun Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba
Domin Kari