Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Fiye da Mutane Goma Tare da Sace 'Yansanda a Ibi Jihar Taraba


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Hukumomi a jihar Taraba sun tabbatar da kashe mutane fiye da goma a Ibi tare da sace wasu 'yansanda biyu da mata da yara da jirgin ruwan kwale-kwale da suke ciki

Maharan sun tare jirgin ne yayin da yake dauke da 'yan kasuwa ta kan hanyarsu zuwa cin kasuwar garin Tella.

Ana zargin cewa maharan sun fito ne daga wasu yankunan jihar Filato sun yi diran mikiya ne a garuruwan Mala da Dampar dake cikin karamar hukumar Ibi.

Kawo yanzu ba'a san adadin mutanen da abun ya shafa ba. Wani da ya zanta da wakilin Muryar Amurka ya yi zargin cewa Yargamawa da Jukunawa suna cikin garin Mala. Ba'a san ko mutane nawa suka kashe ba. Babu jami'an tsaro a garin. Wai sun je garin kwana daya kawai kana suka fice. Ya kara da cewa Yargamawa sun kwace jirgin da zashi kasuwar Tella daga Dampar.

Maharan sun kai hari akan jirgin lokacin da yake kan ruwa. Maharan sun yi ma jirgin kwantan bauna ne. Da ya iso inda suka labe a bakin gabar ruwa sai suka bude masa wuta. Mazan dake ciki sun tsunduma cikin ruwa amma mata da yara da wasu 'yansanda biyu da zasu karbar albashinsu, 'yan bidigan sun yi awon gaba dasu.

Shugaban karamar hukumar Ibi Isiyaka Adamu ya tabbatar da harin. Ya kuma nuna damuwa da yadda yankin ke nema zaman tungar 'yan hare-hare. Yace abubuwan dake faruw a yankin Dampar ba na yau ba ne. Yankin ya dade yana fama da hare-hare. Sai bayan binciken jami'an tsaro ne za'a iya gane ko mutane nawa ne suka halaka da kuma dukiyoyin da suka salwanta.

To sai dai shugabannin al'ummar Yargamawa sun musanta zargin cewa su ne suka kai hari. Shugaban kabilar na karamar hukumar Ibi yace basu ne suka kai hari ba. Yace wadanda ma aka koresu daga gidajensu fiye da mutane dubu daya suna tare dasu sun basu mafaka sabili da haka babu yadda zasu kaiwa kowa hari.

Yanzu dai an tura karin jami'an tsaro a yankin domin a kwato wadanda maharan suka yi awon gaba dasu. Kakakin 'yansandan jihar Taraba ASP Joseph Kwaji yace 'yanbindiga sun shigo ne daga Filato. Ba'a san ko su wanene ba. An tura 'yansanda da 'yansandan kwantar da tarzoma su nemesu kana su kwatosu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG