WASHINGTON, DC —
Wasu shugabannin kananan hukumomin jihar Taraba cikinsu ya duri ruwa sanadiyar barazanar da kansiloli ke yi masu na neman tsigesu daga mukamansu.
Barazanar dai ana kwatantata da dambarwar dake tsakanin mukaddashin gwamnan jihar da wasu 'yan jihar dake majalisun tarayyar Najeriya. Ana raderadin cewa 'yan majalisun suna neman takawa mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umaru birki ne wanda yake kokarin tsayawa takarar zaben gwamnan jihar a shekarar 2015.
Guguwar tsige shugabannin kananan hukumomi tuni ta kada zuwa cikin karamar hukumar Ibi dake kudancin jihar. Kansaloloin karamar hukumar sun mikawa shugaban hukumar takardar neman tsigeshi.
Kakakin karamar hukumar Sanusi Muhammed Sambo yace suna tuhumar shugaban hukumar da aiwatar da aiki ba bisa kan doka ba. Akwai wasu taruka da ya kamata yayi tare da kansalolin ayyuka da daraktocinsa amma suna zargin cewa tun da shugaban ya hau kujerar bai taba yin taro da kowa ba. Dalili ke nan bisa ga tsarin doka suka jawo hankalinsa. Sambo yace sun bashi shawara ta baka da baka bai yi komi ba. Sun rubuta masa amma bai kula ba. Yace to yanzu lokaci yayi da zasu dauki mataki.
A siyasance 'yan majalisun tarayya suna ganin mukaddashin gwamnan yana samun goyon bayan shugabannin kananan hukumomi sabili da haka suka shirya tsigeshi ta yin anafani da kansiloli. To amma tuni kansilolin suka musanta zargin. Kansilo Tasiu Abdulkarim Magaji mai wakiltar Rimi Uku yace har ga Allah babu wanda ya sasu su nemi tsige shugaban karamar hukumarsu. Suna yi ne tsakaninsu da Allah kuma domin mutane.
A wani halin kuma shugaban karamar hukumar Ibi Isiyaka Adamu ya musanta zargin kansilolin inda yace wani ne yake son yayi anfani da su. Ya kuma ce shi bai samu wata takarda daga kansalolin ba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.