Majalisar na son likitoci su fada mata gaskiya dangane da lafiyar gwamna Danbaba Suntai kamar yadda kundun tsari ya tanada domin kawo yanzu watanni ashirin da biyu ke nan baya bakin aikinsa.
Akan binciken kakakin majalisar zai kafa kwamitin likitoci biyar da zai hada da likitan dake kula da gwamnan domin ya bada rahoton da majalisa zata yi aiki dashi.
To amma mukarraban gwamna Danbaba Suntai, wanda yanzu yana jinya a kasar waje, sun mayar da martani akan matakin da majalisar ke son ta dauka. Suna zargin da wata manufa majalisar ta dauki matakin.
Eammanuel Bello tsohon kwamishanan yada labarai kuma wanda yayi adabo da mukaddashin gwamnan jihar yace ana jinyar mutum kana a ce ba zai dawo ba. Wai tun ranar da gwamnan ya samu hatsari mukaddashin wanda a lokacin shi ne mataimakin gwamnan yake neman ya maye gurbin gwamnan. Wai dalili ke nan da ya saukar da duk kwamishanonin da suka yi aiki da gwamna Danbaba.
Mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar ya mayar da martani ta bakin jami'insa na yada labarai Mr. Aaron Atima wanda yace a wurin wanene za'a kwace mulki. Gwamnatin daya ce, wato gwamnatin Danbaba Suntai. Babu wata kuma. Shi mukaddashin gwamnan jihar bai taba yin wani abu da ya sabawa gwamnatin Danbaba Suntai ba. Shirin da ya bari ne mukaddashin gwamnan ke bi.
Idan za'a bi gaskiya kowane dan Taraba yana da hakin ya san halin da gwamnansu yake ciki. Ba'a ce ya bar kujerarsa ba. Ba'a ce a jireshi daga mulki ba amma a bi tsarin kundun mulkin kasa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.