Akwi alamar tambaya dangane da abun da ya faru a Cibok domin sabili da tsoron kada 'yan Boko Haram su kai hari akan makarantun gwamnatin jihar ta rufesu. Da zata kirawo yaran domin yin jarabawar kammala karatun sakandare, meyasa ba'a shirya masu ingantacen tsaro ba?
A wani yunkuri na kawar da rudani bisa ga ikirarin da aka ce sojoji sun yi dangane da daliban da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a Chibok, hukumomin jihar Borno sun jaddada cewa kawo yanzu dalibai ashirin ne kawai aka gano.
Yayin da ake raderadin cewa za'a sake kai hare-hare akan Abuja ministan birnin Bala Mohammed ya tabbatar da kara daukan matakan karfafa tsaro a birnin.
An zargi gwamnati jihar Yobe da da rashin taimakawa iyayen yaran da suka bace a makarantar Buni Yadi a kwanakin baya, lokacin da 'yan bindiga suka kai hari makarantar har suka kashe dalibai da dama.
Bayan sun kammala taron majalisar zartaswa ta Najeriya ministan yada labarai ya fadawa manema labarai cewa tuni shugaban kasa ya umurci jami'an tsaro su kubutarda yaran da aka sace a Chibok jihar Borno.
Daren Laraba mazauna garin Misau a jihar Bauchi sun kwana cikin tsoro da firgita sanadiyar hare-harbe na bindigogi da kuma tada bamabamai.
Wani sanata dake kan gaba wurin gabatar da kudurori a majalisar dattawa yace ba zasu amincewa da sake sabunta dokar ta baci ba
Kungiyar gwamnonin arewa ta fitar da wata sanarwa inda tayi tur da harin da aka akan Nyanya wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikata wasu masu yawa.
Yayin da Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya zanta da gwamnan Borno dangane da yara mata da aka sace daga makarantarsu dake Chibok, gwamnan ya bada tabbacin cewa sun dauki matakan gano yaran da nufin kubutarda su.
Bayan fitowar rade-radin wani sabon harin, an kara tsaro a babban Birnin Tarayya Abuja yanzu bayan fashewar boma-bomai a tashar motar Nanya da yayi sanadiyar rasa rayuka misalin 75 da jikkata sama da mutane 100 da kuma asarar dukiyoyi Litinin dinnan.
Gwamnatin jihar Borno ta ce zata bayar da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka samo dalibai mata su kusan 200 da aka sace su daga Makarantar Sakandaren garin Cibok.
Gwamnatin jihar Taraba ta kafa dokar hana fita dare da rana a garin Wukari biyo bayan wani sabon rikici da ya barke a garin.
Domin Kari