WASHINGTON, DC —
Ministan birnin Abuja Sanata Bala Mohammed ya sake jaddawa a bainar jama'a cewa ana karfafa matakan tsaro a birnin.
A daidai lokacin da mahukuntan Najeriya ke kokakrin gano wadanda suke da hannu a harin da aka kai akan Nyanya da ya kashe mutane da dama da kuma jikata wasu masu dimbin yawa, ministan babban birnin tarayya Sanata Bala Mohammed yace ma'aikatarsa na daukan duk matakan da suka wajaba domin a tabbatar an kara kare Abuja ganin yadda 'yan ta'ada ke kara auna harinsu akan manyan birane da kuma wurin dake da cunkoson jama'a.
Wannan bayanin na ministan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta yin korafi a cikin Najeriya cewa gwamnatin kasar tana kashe makudan kudade wurin samarda tsaro amma babu kayan aiki da naurori irin na zamani na bincike-bincike da zasu taimakawa jami'an tsaro wurin gudanarda ayyukansu.
Sanata Bala yace akan matakan tsaron Abuja an yi takatsantsan kwarai da gaske domin shekara biyu ke nan 'yan ta'ada na kokarin shiga su kuma suna kokarin tsarewa kodayake tsaro na hannun Allah Mahaliccinmu. Yace a cigaba da addu'a kuma mutanen gari su san cewa basa barci. Yace wasu rushe-rushe da suka yi sun ta'allaka ne akan irin labarun da suke samu. Misali a Nyanya da akwai mutane sun fi dubu goma da suke gindin gada. Sabili da abubuwan da suka ji yasa suka share wurin. Lokacin da suka yi hakan mutane suna ta kuka domin basu san dalilin da yasa suka yi hakan ba.A wurin suka kafa tashar motoci domin ta taimakawa mutane masu kai da kawowa tsakanin Nyanya da birnin tarayya.
Gwamnati zata yi kokari ta sa naurori a duk tashoshinta. Za'a kuma kara 'yan sanda masu sa fararen kaya domin su dinga kula da masu shiga da fita. Za'a sa naurorin leke a tashoshi da kasuwanni da asibitoci. Gwamnati zata yi kokari ta tatabbatar babu wani dan ta'ada da zai shigo da mota da bam ya ajiye.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.