WASHINGTON, DC —
Yayin da aka samu kwanciyar hankali a Ibi sai ga garin Wukari ya fada cikin dokar hana fita dare da rana sanadiyar barkewar wani sabon rikici.
Rahotanni sun tabbatar da kafa dokar hana fita ba dare ba rana a garin Wukari sanadiyar barkewar wani sabon rikici. Rikicin ya barke ne bayan da matasan jukunawa suka dauko gawar wani fitacen mayakinsu da aka kashe a wata arangama da ta auku ranar Talata a kauyen Wunco a yankin Jibo. Amma duk da dokar hana fita an kwana ana ta harbe-harbe cikin dare.
Kawo yanzu ba'a san adadin wadanda aka kashe ba ko kuma aka raunata. Fadan ya samo asali ne a kauyen Wunco inda aka kashe babban mayakin jukunawa. Matasan jukunawan suna dawowa sojoji suka hanasu shiga gari. Daga wurin matasan suka koma kasuwar doya suka shiga dukan mutane suna fasa kawunan wasu. Akwai labarin dake cewa sun kashe mutane da dama.
Duk da cigaba da harbe-harbe mazauna garin na Wukari sun ce basu ga alamar sojoji ba. Wani yace 'yan sandan kwantar da tarzoma da suka je anguwar hausawa sai suka kama harbi lamarin da ya sa matasan hausawa su ma suka fito da shiri. Daga nan aka karya dokar hana fita.
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da halin da ake ciki gameda sabon rikicin da ya barke a garin Wukari. ASP Joseph Kwaje kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar da lamarin. Yace matasan jukunawa suka tashi yin zanga zanga sai jami'an tsaro suka fatattakesu suka watse. Yanzu dai suna sintiri ciki da kewayen garin.
Gwamnatin jihar Taraba ta bakin sakataren yada labaran mukaddashin gwamnan Mr. Kefas Sule yace an kafa dokar hana fitan ne domin kare rayuka. To sai dai harin sari ka noke yana cigaba tsakanin jukunawa da tibabe da fulani makiyaya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.