WASHINGTON, DC —
Shugaban kasar Najeriya ya baiwa jami'an tsaron kasar umurnin su gano inda yara mata da aka sace daga Chibok suke su kuma kubutarda su.
Shugaban kasar Najeriya ya bada tabbacin baiwa jami'an tsaro su binciko wadanda suka sace yara mata daga makarantarsu dake garin Chibok a jihar Borno su kuma kubutarda su.
Bayan da majalisar zartaswar kasar ta gama taronta a Abuja ministan labarai Labaran Maku yayi bayani. Yace jami'an tsaro suna aikinsu domin a ganosu a kuma mayarda su gidajen iyayensu. Shugaban kasa ya riga ya bayarda umurni kuma ana kan yin aikin. Yayi addu'ar Allah Ya bada nasara akan miyagun mutanen dake muguwar aika-aika. Yace mutanen sun watsar da duk dokokin Allah na kowane addini. Babu shakka shedan su ke yiwa aiki. Yace babu wani addini da yace a kama yara mata a shiga daji da su.
Da wakilin Muryar Amurka ya gayawa ministan cewa abun mamaki ne a ce 'yan bindiga sun shiga makarantar sun yi sa'o'i hudu suna kama yara suna sasu cikin motoci amma babu ko jami'in tsaro daya da ya je wurin, sai ministan yace rahotannin da 'yan jarida ke ji ke nan.
Ministan ya juya kan 'yan jarida inda yace labaran da suke bayarwa sukan karya gwiwar jami'an tsaro. Yace suna magana ba tare da tabbatar da an samu zaman lafiya ba. Yace yayin da suke magana wasu suna daji kuma ta yiwu su rasa rayukansu domin a samu zaman lafiya. Sojoji da 'yansanda babu ranar da ba sa rasa mutum.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.