WASHINGTON, DC —
Bayan taronta kungiyar gwamnonin arewa ta fitar da wata sanarwa inda tayi tur da harin da aka kai a kan Nyanya kusa da Abuja safiyar Litinin da ta gabata.
A sakamakon harin da aka kai akan Nyanya da ya hallaka mutane da dama kungiyar gwamnonin arewa ta fitar da wata sanarwa da tayi allawadai da harin. A cikin sanarwar gwamnonin sun jajantawa wadanda harin ya shafa. Ta kuma kira jami'an tsaron Najeriya da su kara himma.
Alhaji Danladi Ndayabo kakakin shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu yace sun nemi jami'an tsaro su kara himma kuma sun jaddada maganar tsaro ba ta jami'an tsaro ba ce kawai, ta kowa da kowa ce. Gwamnonin sun bukaci jama'a kowa yayi takatsantsan ya lura da inda yake domin a tabbatar an kawo karshen wannan ta'asar.
Dangane da ko gwamnonin sun tanadi wani taimako ma wadanda abun ya rutsa da su sai Ndayabo yace duk lokacin da irin wannan abun ya faru gwamnoni sukan kebe wasu kudade na tallafawa wadanda lamarin ya shafa.
Gwamnonin basu fitar da wata sanarwa ba akan 'yan matan da aka sace daga makarantarsu dake Chibok. To saidai batun yaran na cigaba da daukar hankali.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Neja Nuradeen Umar ya kira 'yan Najeriya cewa kowa ya dukufa da addu'a Allah Ya kawo ma kasar sauki dangane da abun dake aukuwa. Yayi fatan Allah Ya sa a samu yaran da aka sace kuma a samesu cikin lafiyarsu. Yace mafita ita ce gwamnati ta tashi da gaske ta nemesu. Yace tayin tukuicin da gwamnan jihar Borno yayi alama ce da nuna yana cikin bakin ciki da abun da ya faru.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.