Kwana daya bayan tashin bamabamai biyu a garin Kaduna sai gashi wani ya sake fashewa a wata tashar mota a Sabon Garin Kano jiya.
A cikin firar da yayi da Muryar Amurka Shaikh Dahiru Bauchi ya bayyana irin kokarin da yayi na kawo sulhu tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar Boko Haram amma wasu jami'an gwamnati suka sa kafafu suka shure shirin
Gwamnatin jihar Kaduna tayi bayanin dalin kafa dokar hana fita dare da rana a wasu kananan hukumomin jihar biyo bayan tashin bamabamai biyu a birnin Kaduna.
Yayin da ake rufe tasirin azumin wannan shekarar a Sokoto kungiyar IZALA tayi tur da hare-haren bamabamai da aka kai a Kaduna.
A firar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto Janaral Buhari ya bayyana yadda aka kai hari a kan tawagar motocinsa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura.
Akalla mutane 25 suka mutu wasu da dama kuma suka jikita.
Hukumar yake da almundahana wato EFCC tana neman tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako,
Yayin da aka cika kwanaki dari da sace 'yan matan makarantar sakandare dake garin Chibok jihar Borno daliban sakandare a jihar Neja sun gudanar da addu'o'i na musamman Allah Ya kubutar da 'yan matan.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sadu da iyayen 219 na ‘yan matan da aka sace a garon farko da wasu da suka samu kubuta a Abuja. Jonathan yayi alkawarin kubuto da sauran da ransu ta bakin mai Magana da yawun shi Reuben Abati.
Yau ya cika kwanaki dari da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Gombe ta samu 'yan gudun hijira da dama daga Damboa jihar Borno wadanda suke gujewa hare-haren da 'yanbindiga ke kai masu ba kama hannun yaro
Domin Kari