Bamabaman da suka fashe a Kaduna sun hallaka akalla mutane tamanin amma ba'a san adadin na Kano ba kawo yanzu.
Tashar motar dake New Road tasha ce inda ana daukar fasinjoji dake balaguro zuwa sassan kudancin Najeriya. Bam din ya fashe ne a cikin wata mota kirar safa wadda ana sa mata fasinjoji da zasu birnin Fatakwal.
Wani ganao ya bada karin haske. Yace yana jin akwai wadanda suka mutu a cikin motar wasu kuma sun jikata. Amma tuni kwamishanan 'yansandan jihar Kano Mr Adelere Chinapa ya ziyarci wurin jim kadan bayan faruwar lamarin.
A zantawar da yayi da manema labarai kwamishanan yace abun da aka sanar dasu motar tayi lodi ne zuwa birnin Fatakwal kuma daga cikin kayan da aka sanya mata a kwai naurar sanya ababen sha ta firiji. Ana zaton a cikin firijin ne aka makala bam din. Kwamishanan ya tabbatar da mutuwar mace daya kuma mutane takwas sun jikata an kuma kaisu asibiti.
Shi kuwa shugaban kabilar Igbo a Kano yace a madadin al'ummarsa da al'ummar Kano gaba daya yana bayyana alhini dangane da wannan aikin rashin imani. Ya kira jama'a da su kula sosai da abubuwan dake kai kawo a tsakaninsu. Yace tilas ne kuma gwamnati ta kara kaimi wajen kawo karshen wannan matsala. Yace kodayake hukumomi sun ce suna hobbasa amma kokarin nasu bai kai inda ya kamata ba.
Wannan shi ne karo na biyu cikin shekaru daya da rabi da bam ya fashe a tashar motar.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.