Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya yace a shirye yake ya shiga tsakani, a nemi zaman tattaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram, domin kawo karshen tashe-tashen hankula dake faruwa a wasu jihohi dake arewa maso gabashin Najeriya, da ma wasu bangarorin kasar.