Bishop Stephen Damin Mamza ya bayyana irin halin da suke ciki.
Yace akwai kauyuka da yawa a jihar Adamawa da 'yan kungiyar Boko Haram suka kori mutane wadanda yanzu babu inda zasu je. Akwai wasu kuma da yawa da suna neman abinci da wurin tsugunawa. Suna cikin Yola ko Kamaru.
Dalilin bayanin da Bishop Mamza ya bayar, wakiliyar Muryar Amurka ta tuntubi dan majalisar dattawa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya domin jin ko shugabannin hukumomin tsaro suna bayyanawa majalisar halin da ake ciki kamar yadda suka nema a lokacin da suka sake sabunta dokar ta bacin.
Sanata Gaya yace ganin abun da ya faru ya kira shugaban majalisar David Mark ya fada masa babu anfanin su tafi hutu kasa bata da lafiya. Ya bukaci a yanke hutun su koma su zauna a majalisa domin yakamata shugabannin tsaro su basu bayanai akan abubuwan da suka yi a watan farko. To amma daidai watan farkon sai aka rufe majalisa.
Sanata Gaya yace a yanke hutun su koma su zauna domin yin nazari akan abubuwan dake faruwa. Ko menene za'a yi domin a samu zaman lafiya a kasar ya zama wajibi a yi. A lokacin marigayi shugaba 'Yar'adua sun yanke hutu domin abubuwan da suka kunno kai kodayake ba'a rasa rayuka can lokacin balantana yanzu da aka kashe dubban mutane. Saboda haka lallai ne a kira zama ciki gaggawa. Sanata David Mark yayi alkawarin tuntubar shugabannin majalisar domin su kira taron na gaggawa. Wajibi ne su dauki matakin da ya dace kowane iri ne domin a cimma zaman lafiya.
Amma kuma Aliyu Ibrahim Gebe yace labarin ya banbanta a bangarensu na majalisar wakilai domin shugabannin hukumomin tsaron suna zuwa su yi masu bayani amma ba a zaman majalisar gaba daya suke shigowa ba. Suna saduwa ne da kwamitoci musamman kwamitin dake da hurumin sa ido a ayyukansu. Kwamitin yana da mutane talatin da shida wato mutum daya daga kowace jiha. Idan sun hadu sai kowane dan kwamitin ya nemi 'yan jiharsa ya basu kwapi. Daga nan sai su dauka su gayawa al'umma. Idan ya kama su gayawa majalisar a dunkule sai su yi hakan. Yace sai dai abubuwa da suka shafi harkar tsaro ba lallai ba ne a fito ana fada a bainar jama'a ba.
Ibrahim Gebe yace ana samun cigaba. Matsalar ba rana daya aka shigeta ba kuma canji ba'a samunsa rana daya.
Ga rahoton Medina Dauda.